Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : kasar Iran ya nakalto Bakiri ya na fadar haka a dai dai lokacinda tattaunawar Vienne ke karatuwa. Dangane da bukatar kasashen yamma na a fara tattaunawar ta Vienna daga inda aka tsaya a tattaunawar karshe, Bakiri ya ce, babbar matsala a wajen Iran itace takunkuman da Amurka ta dorawa kasar, da kuma matsalolin da ficewar Amurka ya jawowa yarjejeniyar JCPOA.
Ali Bakiri ya kammala da cewa Amurka ce ta fice daga yarjejeniyar, Iran tana cikinta, don haka abu na farko da Amurka za ta yi idan tana son dawowa cikin yarjejeniyar, shi ne ta dage wadannan takunkuman da ta dorawa Iran, sannan sai Iran ta tabbatar an dage takunkuman da gaske, sanann ta koma inda take kafin ficewar Amurka.
342/